(ḥawsa) حَوْسَ
Muna gayyatar kamfaninku ya aiko zabukansa na Stevie® Awards for Sales & Customer Service na shekarar 2025 (shekararsa ta 19). Gasar girmamawa ajin farko a duniya ta ma’aikatan kula da abokan ciniki, masu bunkasa kasuwanci da kwararru a fannin cinikayya na zuwa muku ne daga wadanda suka kirkiri International Business Awards® da American Business Awards® masu daraja.
Idan kuna son a aiko muku takardun shiga gasar, mai dauke da kaidojin yadda za a shiryawa shiga gasar da kuma mika cikakkun takardun shiga gasar, sai ku shighar da adireshin imel dinku a nan, mu kuma za mu aiko muku su ta imel. Muna da tsarin tsare-sirri mai karfi kuma ba za mu bawa kowa adireshin imel dinku ba saboda kowanne dalili.
Wannan shafin shi ne kadai za ku gani a wannan shafin na intanet a cikin wannan harshen. Dukkan sauran shafukan suna kunshe ne da bayanai cikin turancin Ingilishi, kamar su ma takardun shiga gasar. Hakan ta faru ne saboda mun bukaci da a gabatar da bukatar shiga gasar cikin turancin Ingilishi, domin kwararru kan harkokin kasuwanci a duk fadin duniya su taka rawa wajen tantance wadanda suka shiga gasar.
Stevie Awards for Sales & Customer Service na girmama ci gaban ma’aikatan kula da abokan ciniki, masu amsa wayoyin abokan ciniki, masu bunkasa kasuwanci da kwararru a fannin cinikayya na duniya baki daya. Kungiyar shirya gasannin ta Stevie Awards, wacce take bada lambobin yabon, mazauninta na Amurka. Sune masu shirya gasannin Cin Lambobin Yabo ta Stevie Awards daban daban guda takwas wanda za ku iya samun bayani game da su a www.StevieAwards.com . Gasar cin lambar yabo ta Stevie Awards ta zama daya daga cikin lambobin yabo na duniya da ake girmamawa.
A shekarar 2024, an bada Stevie Awards for Sales & Customer Service ga kamfanoni da mutane daga kasashe sama da 40 a wani taron cin abinci da aka yi a Las Vegas, Nevada U.S.A. Latsa nan domin ganin jerin wadanda suka yi nasara a zangon 2024.
Akwai ire-iren rukunonin lambobin yabo da za a iya zaba a Stevie Awards for Sales & Customer Service. Idan kuka zabi shiga gasar, za ku zabi rukunin da ya dace da nasarorinda kungiyar ku ta samu kuma take son a karrama ta a kai, ku kuma shirya takardun shiga gasar bisa kaidojin da aka gindaya. Rukuni-rukunin gasar da ake da su, sun hadar da :
- Cinikayya
- Jami’an Cinikayya
- Tawagar Cinikayya
- Ci Gaba a Cinikayya
- Kwarewa a Cinikayya
- Kula da Abokan Ciniki Da Amsa Wayoyin Abokan Ciniki
- Kula da Abokan Ciniki Da Jami’in Amsa Wayoyin Abokan Ciniki
- Kula da Abokan Ciniki Da Tawagar Amsa Wayoyin Abokan Ciniki
- Kula da Abokan Ciniki Da Ci Gaba a Amsa Wayoyin Abokan Ciniki
- Bangaren Kula da Abokan Ciniki
- Nasarorin Kula da Abokan Ciniki
- Sabon Abun Sayarwa da Sabis
- Mai Bada Mafita
- Bunkasa Kasuwanci
Jeri da bayanan rukunonin ya na cikin takardun shiga gasar.
Zabukan na bukatar a aika rubutacciyar makala ko nazari mai kalmomi da suka kai 650 da ke bayyana nasarorin da wanda aka zaba ya samu a lokacin cancanta, ko kuma za a iya aika bidiyo mai tsahon mintina biyar (5) inda za a bayana nasarorin wanda aka zaba. Wanda aka zaba yana iya zama mutum daya, wata tawagar, sabon samfurin, wani sabis, ko kuma duka kungiyar.
Za a sanar da lambar yabo ta 2025 Stevie Awards a cikin nau'ikan tallace-tallace da sabis na abokin ciniki a ranar 6 ga Maris. Za a gane masu cin nasara a wani biki a birnin New York ranar 10 ga Afrilu. Ba a buƙatar masu cin nasara su halarci bikin.
Lambar Yabo ta Stevie Awards na da wakilai a kasashe da dama. Wadannan wakilai za su raba bayanai su kuma taimakawa kamfanoni a kasashensu wajen shiga gasar cin lambar yabon.
Domin tantancewa ko akwai wakili a kasar ka, latsa nan.
Za ku kuma iya tuntubar masu shiryawa a wannan adireshi mai zuwa:
The Stevie Awards
10560 Main Street, Suite 519
Fairfax, Virginia 22030, USA
Lambar Waya: +1 703-547-8389
Fax: +1 703-991-2397
Imel: help@stevieawards.com