Search our sites

Search past winners/finalists


  • MESA logo
  • SATE logo

(ḥawsa) حَوْسَ

IBA Montage

Muna gayyatar kungiyar ku da ta gabatar da bukatar shiga gasar cin Lambar Yabo ta Stevie® ta shekarar 2025 (karo na 22) ga mata ‘yan kasuwa.  Shirin nan babbar lambar yabo a fagen kasuwanci ta duniya ta musamman ga mata, kirkira ce ta gasannin cin lambar yabo ta duniya mai alfarma, da kuma Gasannin cin lambobin yabon kasuwanci na Amurka.

Idan kuna son a aiko muku takardun shiga gasar, mai dauke da kaidojin yadda za a shiryawa shiga gasar da kuma mika cikakkun takardun shiga gasar, sai ku shighar da adireshin imel dinku a nan, mu kuma za mu aiko muku su ta imel. Muna da tsarin tsare-sirri mai karfi kuma ba za mu bawa kowa adireshin imel dinku ba saboda kowanne dalili.

 

Wannan shafin shi ne kadai za ku gani a wannan shafin na intanet a cikin wannan harshen. Dukkan sauran shafukan suna kunshe ne da bayanai cikin turancin Ingilishi, kamar su ma takardun shiga gasar. Hakan ta faru ne saboda mun bukaci da a gabatar da bukatar shiga gasar cikin turancin Ingilishi, domin kwararru kan harkokin kasuwanci a duk fadin duniya su taka rawa wajen tantance wadanda suka shiga gasar.

Game da Stevie Awards for Women in Business (Lambobin yabo na Stevie ga mata ‘yan kasuwa)

Gasar cin lambobin yabo na Stevie ga mata ‘yan kasuwa na karama nasarori da mata ‘yan kasuwa, da shugabanni, da ma’aikata da kungiyoyi da suke gudanarwa suka samu a duk fadin duniya.  Kungiyar shirya gasannin ta Stevie Awards, wacce take bada lambobin yabon, mazauninta na Amurka. Su ke shirya gasannin Stevie daban-daban har guda takwas wadanda za ku iya samun karin bayani a kansu a www.StevieAwards.com.  Gasar cin lambar yabo ta Stevie ta zama daya daga cikin lambobin yabo na duniya da ake girmamawa.

A shekarar 2024, an bada lambobin yabo na Stevie ga mata ‘yan kasuwa ga kungiyoyi da daidaikun mutane daga fiye da kasashe 30. Danna nan don ganin jerin waɗanda suka yi nasara a bugun 2024.

Rukuni-Rukuni

Akwai rukuni-rukuni da dama na lambobin yabon da za a iya zaba daga cikin gasar cin Stevie Awards for Women in Business (lambobin yabon Stevie ga mata ‘yan kasuwa). Idan kuka zabi shiga gasar, za ku zabi rukunin da ya dace da nasarorinda kungiyar ku ta samu kuma take son a karrama ta a kai, ku kuma shirya takardun shiga gasar bisa kaidojin da aka gindaya. Rukuni-rukunin gasar da ake da su, sun hadar da :

  • Rukunin lambobin yabo na daidaikun mata ya kunshi  
    • Gwarzuwar Mace ‘Yar Kasuwa ta Shekara
    • Gwarzuwar Mace Mai Kirkire-Kirkire ta Shekara
    • Gwarzuwar Mace Mai Shugabanci ta Shekara
    • Gwarzuwar Mace Ma’aikaciya ta Shekara
  • Rukunin Lambobin Yabo na Kamfani ko Kungiya (Da Mace ta Mallaka ko take Jagoranta)
  • Rukunin Lambobin Yabo na Sabon abin da aka kera ko hidima (Da aka Samar don Mata/Mata suka samar)
  • Rukunin Lambobin Yabo na Sadarwa ko tallata kasuwanci (Da aka Samar don Mata/Mata suka samar)
  • Rukunin Lambobin Yabo na Sauti ko Hoton Bidiyo (Da aka Samar don Mata/Mata suka samar)
  • Rukunin Nasarori
  • Rukunin Social Media
  • Rukunin Thought Leadership

An bayyana jerin sunaye, da bayanan rukuni-rukuni, da abubuwan da ake bukata wajen gabatar da bukatar shiga gasar, da lokacin rufe shiga gasar da ma duk wani kudin shiga gasar, a cikin takardun shiga gasar.

Lambobin Yabo

Za a sanar da sunayen wadanda suka yi nasarar kai wa rukunin karshe na lambobin yabo na Stevie ga mata ‘yan kasuwa a ranar 19 ga watan 0Satumba. Bayan haka, za a sanar da wadanda suka lashe kyautar Zinariya, Azurfa da Bronze Stevie a yayin wani liyafar cin abincin dare a birnin New York. Stevie na Zinare, da Azurfa da Tagulla ga wadanda suka yi nasara.

Tuntuba

A tuntube mu da tambayoyi da ake da su game da Stevie Awards for Women in Business (Gasar cin Lambar Yabo ta Stevie ga Mata ‘Yan Kasuwa) ko kuma kowacce daya daga cikin Stevie Awards (gasannin cin lambar yabo ta Stevie).

The Stevie Awards
10560 Main Street, Suite 519
Fairfax, Virginia 22030, USA
Lambar Waya: : +1 703-547-8389
Fax: +1 703-991-2397
I-mel: help@stevieawards.com